Boko Haram: An kafa tutoci a Ashigashiya

Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau Hakkin mallakar hoto AFP PHOTO BOKO HARAM

Rahotanni daga Jihar Borno na cewa wasu 'yan bindiga da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram sun kame garin Ashigashiya dake kusa da garin Gwoza.

Tun a daren litinin ne mazauna garin suka ce aka fara harbe-harbe.

Lamarin na zuwa ne kwana biyu bayan kame garin Gambaru-Ngala mai makwabtaka da Kamaru.

Rahotanni daga garin Mubi a jihar Adamawa a Nigeria na cewa sojojin kasar kimanin 480 da suka tsere zuwa Kamaru sun isa garin na Mubi cikin yanayi na gajiya da kuma yunwa.

Wani mazaunin garin na Mubi ya ce ya ga sojojin a lokacin da ake sauke su a motoci wasu na dauke da makamai wasu kuma babu, yayin da wasu ke tafe da motoci masu sulke. Maudu'o'i masu alaka

Wasu bayanan kuma sun ce an bai wa sojojin wadanda wasunsu ke sanye da kakin soji wasu kuma ke sanye da singileti abinci a wani sansanin soji da ke garin na Mubi.

A ranar Litinin ne dai rundunar sojin Najeriya ta ce ta cimma fahimtar juna da Kamaru kan dawowar sojojin gida.

Inda a sanarwar da ta fitar ta ce shiga cikin Kamaru da sojin Najeriyar suka yi dabarar yaki ce kawai ba tserewa suka yi ba.

Lamarin ya biyo bayan kazamin fadan da aka yi ne tsakanin 'yan kungiyar Boko Haram da kuma sojojin Najeriyar a garin Banki da ke bakin iyaka a karshen mako.

Karin bayani