Gwamnati ta yi watsi da shelar Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP PHOTO BOKO HARAM
Image caption Sai dai sanarwar Boko Haram ba ta fayyace ko daular musulunci ta kungiyar Isis ba ko kuma wata daban

Gwamnatin Nijeriya ta yi watsi da shelar shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau da ke cewa garin Gwoza na cikin jihar Borno, da ke hannun kungiyarsa ya koma karkashin daular Musulunci.

Martanin gwamnatin Nijeriya ya zo ne kwana guda bayan shugaban Boko Haram ya fitar da wani hoton bidiyo inda a ciki ya yi ikirarin cewa gwoza ya zama wani bangare na daular musulunci.

Ministan yada labaran kasar, Mr. Labaran ya ce babu wani bangaren iyakar kasar da zai zama cibiyar gwaji ta kafa daular 'yan ta'adda a Afirka ta yamma, ya ce gwamnati tana da kwarin gwiwa a kan karfin sojan kasar wajen tsarewa da kare martabar iyakokin Nijeriya.

Mr. Maku ya ce 'yan Nijeriya da wasu mutane daga waje da ke yunkurin kawo nakasu ga hadin kan kasar, su kwan da sanin cewa gwamnati za ta kare Nijeriya da duk karfinta.

Ya ce Nijeriya za ta ci gaba da zama jagora a nahiyar Afirka.