Ebola: Mutum daya ya rage a killace

Hakkin mallakar hoto
Image caption Akwai bukatar taka tsatsan wajen lura da masu cutar Ebola

Gwamnatin Nigeria ta ce mutum daya tal ne ya rage a cibiyar killace masu dauke da cutar Ebola bayan da aka sallami wasu daga cikin wadanda suka warke daga cutar.

Ministan Lafiya a kasar, Dr Onyebuchi Chukwu ya bayyana haka ne bayan da ya sanar da sallamar mutane biyu wadanda suka warke daga cutar.

A cewar sa, mutane 13 ne suka kamu da cutar Ebola a Nigeria, ciki hadda dan Liberia, Patrick Sawyer wanda ya shigo da cutar a cikin kasar a ranar 20 ga watan Yuli kuma ya rasu bayan kwanaki biyar.

Dr Chukwu ya kara da cewar a yanzu mutane bakwai ne suka warke daga cutar a yayinda cutar ta hallaka mutane biyar a cikin kasar.

Cutar Ebola ta kashe mutane 1,400 a kasashen Guinea da Liberia da kuma Saliyo.

Karin bayani