An kashe 'Yan Boko Haram a Kamaru

'Yan Boko Haram Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko Haram

Rohotanni daga Kamaru na cewa jami'an tsaron kasar sun yi bata kashi da wasu 'yan binduga da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne.

Rahotanni na cewa yawan wadanda aka kashen zasu kai ashirin da bakwai.

Lamarin ya faru ne a garin Fotokol lokacinda 'yan bindigar suka yi yunkurin karya wata gada da ta hada Najeriya da Kasar ta Kamaru.

Dakarun Nijeriya su kimanin dari biyar sun koma gida daga Kamarun bayan da suka tsallaka can daga Gamboru Ngala a sakamakon artabu da 'yan Boko Haram da suka kame garin.

Rundunar sojin ta ce sojojin sun shiga Kamaru ne a matsayin dabarar yaki, ba tsere wa abokan gaba ba kamar yadda ake ta fadi.