Ba za mu hana IS amfani da shafinmu ba

Kungiyar sada zumunta ta baki dake zaune wasu kasashe Hakkin mallakar hoto none
Image caption Kungiyar sada zumunta ta baki dake zaune wasu kasashe

Kungiyar sada zumunta ta mutanen da suka bar kasashensu suke zaune a wasu kasashe da ake kira Diaspora ta ce ba za ta iya hana kungiyar masu fafutukar kafa daular musulunci da a takaice ake kira IS aika sakonni ta shafinsu ba.

Kungiyar ta maida martani ne ga rahotannin dake cewa kungiyar ta IS tana amfani da shafin na ta wajen yada akidoji na tsattsauran ra'ayi.

Kungiyar da ta kafa shafin na sada zumunta da kungiyar IS din ke amfani da shi ta amsa cewar ba za ta iya hana yada akidojin na tsaurin ra'ayi ba.

Kungiyar ta Diaspora kungiya ce da ba ta da wani tsayayyen tushe kuma bayanan ta suna cikin matattarar bayanai ne masu yawa, ba a wuri guda ba, don haka babu wani tsayayyen mutum dake sanya ido a kansu.

Kungiyar IS dai ta koma aika sakonnin ta ne ta shafin Diaspora bayan kamfanin Twitter ya yi kokarin babbake asusun ta.

Wadanda suka kirkiro shafin na Diaspora sun ce sun damu da harkokin kungiyar ta IS.

A can baya kungiyar IS tana amfani da shafin twitter ne da sauran wasu shafukkan, amma a yanzu tana yin kaura zuwa wani shafi da ba ya da shamaki.

Jamei Bartlett wani mai sharhi kan shafin yada zumunta kuma marubuci ya ce "ba makawa da kungiyoyi irinsu IS suka zamo cikin masu amfani da wannan shafi."

"don haka babu wata hanya da manyan Shugabannin da suka kirkiro shafin za su yi amfani da ita don juyawa ko janye wasu sakonni da aka tura a shafin kungiyar."

Wannan zai iya zamowa daya daga cikin dalilan da suka janyo kungiyar IS zuwa shafinmu na sada zumunta.

Karin bayani