Ebola: Ministocin lafiya za su yi taro

Hakkin mallakar hoto
Image caption Cutar Ebola ta kashe mutane a kasashen yammacin Afirka

A birnin Accra na kasar Ghana, ministotin lafiya daga kasashen kungiyar kasuwancin yammacin Afrika wato ECOWAS zasu gudanar da wani taro a ranar Alhamis domin duba yadda za su shawo kan bazuwar da cutar nan ta Ebola ke yi da sauri a yankin.

Shugaban kasar Ghana John Mahamma wanda kuma shine shugaban kungiyar ta Ecowas ne ya kira taron mako guda bayan da gwmnatinsa ta hana gudanar da duk wani taron kasa da kasa a cikin kasar ta Ghana don kauce wa shigar cutar a cikin kasa.

Wannan taro na zuwa ne daidai lokacin da kasashen yankin ke cigaba da daukar matakan kariya daga yaduwar cutar.

Matakin baya bayan nan da Najeriya ta dauka na hana yaduwar cutar shine na kara hutun makarantun firamare da kuma na Sakandare.