An gano yarinyar da aka binne da rai

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption India ta yi kaurin suna wajen cin zarafin 'ya'ya mata ta hanyar fyade da sauran miyagun ayyuka

'Yan sanda a arewacin India suna neman iyayen wata yarinya 'yar shekaru 7 wadda aka binne da ranta amma wani mutum ya hako ta a cikin kabari.

Jami'ai a lardin Sitapur na jihar Uttar Pradesh sun ce an gano yarinyar mai suna Tanu, a raye bayan wani mutumin yankin ya bi sawun wani kuka mai ban tausayi da ya ji a wata gonar Rake, inda kuma ya ga kasa tana motsi.

'yan sanda sun zargi kawu da gwaggon yarinyar wadanda suka yi alkawarin kai ta wajen wasa.

An yi zargin mutanen biyu sun daddaure Tanu ne kafin su cusa ta a Kabari.