Rayuwa da 'yan Boko Haram a Gamborou

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko Haram sun kona kasuwar Gamborou Ngala

Rahotanni sun nuna cewar mazauna garin Gambarou Ngala a jihar Bornon Nigeria sun shiga rana ta uku a karkashin ikon kungiyar Boko Haram.

Tun ranar litinin ne mayakan Boko Haram din suka shiga garin ba tare da wata tirjiya ba gada jami'an tsaro.

Daya daga cikin mazauna garin ya shaidawa BBC cewa yanzu 'yan Boko Haram din sun fara taba mutanen gari sabanin abunda suka fada musu da farko.

Ya ce "Muna cikin wahala da kyar muke ci da sha, babu hanyar fita kuma sun je (Boko Haram) gidan wani malami basu same shi ba, sun je gidan wani kuma suka yanka shi."

A cewar mutumin wanda ba ya son a bayyana sunansa, babu jami'an tsaron Nigeria a cikin garin.

A farkon wannan makon ne Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, ya ya yi ikirarin cewa, garin Gwoza da suka kwace daga hannun dakarun Nigeria, a yanzu ba ya karkashin Nigeria, ya koma karkashin daular musulunci.

A nata bangaren, gwamnatin Nigeria ta ce sanarwar ta Boko Haram shirme ce, kuma kasar tana nan a matsayin kasa guda.

Karin bayani