An cire rigar kariyar Hama Amadou

Hama Amadou
Image caption Shugaban Majalisa dokokin Niger

Wani kwamitin majalisar dokoki a jamhuriyar Niger ya kada kuru'ar amincewa a cire rigar kariyar Shugaban Majalisa dokokin kasar, Malam Hama Amadou.

Hakan dai zai bada damar gudanar da bincike akan wani zargi na fataucin yara da ake yi masa.

Mutane goma 17, ciki har da matan wasu manya manyan yan siyasa ne aka kama a watan Yuni bisa zargin sayo jarirai daga Nigeria.

Amaryar Malam Hama Amadou na daga cikin wadanda aka kame.

Malam Hama Amadou, daya daga cikin shugabannin adawa a jamhuriyar Niger ada na cikin kawance tare da gwamnati gabanin su raba gari.

Tun a bara ne dai ake zaman doya da manja tsakanin bangarori daban daban na siyasa a Jamhuriyar Niger abun da ya kawo karshen gwamnatin gamin gambiza karkashin jagoranci Shugaba Mahaman Issoufou.