An kirkiro 'kwakwalwar mutum- mutumi'

Zata iya gane wanda yake kallon akwatin talabijin

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto,

Zata iya gane wanda yake kallon akwatin talabijin

Masu bincike a Amurka sun kirkiri wata 'kwakwalwar mutum- mutumi' wato Robo Brain a turance da zata iya koyan sabbin abubuwa ta hanyar shiga miliyoyin shafukan Intanet

An tsara kwakwalwar mutum- mutumin ne domin ta tattaro sabbin dabaru na aiki iri- iri da kuma ilmi daga wasu shafuka da suke samar da bayanai ga jama'a irinsu You Tube.

Sauran mutum-mutumin dake fadin duniya kuwa zasu iya samun dukkanin irin bayanan da wannan 'kwakwalwar mutum mutumi' take koya, kuma hakan zai taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu na yau da kullum

Ana kirkirar wata fasaha irin wannan a Turai mai suna RoboEarth

An bayyana RoboEarth a matsayin wani shafi da kowanne mutum- mutumi a duniya yake iya shiga domin samun bayanai

Amma ba kamar RoboEarth ba, 'kwakwalwar mutum- mutumi' wato Robo Brain na iya gina nata fahimtar abubuwa daga bayanan data samu daga Intanet a maimakon dan- Adam ya tsara mata yadda zata yi aiki

Za ta iya gane mai kallon Talabijin

Wannan fasaha da aka kirkira sakamako ne na wani aikin hadin gwiwa tsakanin jami'oin Cornell da Brown da Stanford da California na Amurka, tare kuma da goyan baya daga kamfanoni da suka hada da na google da kuma Microsoft

A watan daya gabata ne dai kwakwalwar Robo Brain ta soma tatsar bayanai daga Intanet

An kuma kirkiri wani shafi a Intanet saboda wannan fasaha da aka kirkiro inda shafin zai rika bada cikakken bayanai game da ilmin da kwakwalwar ta samu

Masu bincike sunce kwakwalwar Robo Brain ba gane abubuwa kadai take iya yi ba amma harda fahimtar yadda za a yi amfani da su dama wasu abubuwa masu wahala da suka hada da harshen da mutum yake magana da shi da kuma dabi'a

Misali zata iya gane wanda yake kallon akwatin talabijin