Hanyoyin guje wa cutar Ebola

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hukumomi a kasashen Afrika sun maida hankali wayar da kan jama'a kan cutar Ebola

Cutar Ebola mai saurin kisa ta hallaka mutane da dama amma kuma ba ta yaduwa ta hanyar iska kamar yadda ake kamuwa da mura. Kwararrun kiwon lafiya sun ba da shawarwari kan yadda mutum zai iya kare kansa:

1. Sabulu da Ruwa

Hakkin mallakar hoto Getty

Wanke hannu a kodayaushe da sabulu, da tsabtataccen ruwa sannan a goge hannu da tawul. Sai dai abin na da wuya a yankunan karkara, inda babu ruwan sha.

Dr Unnis Krishnan ya shaidawa BBC cewar a guji yin musabaha da hannu, saboda cutar Ebola ta fi saurin yaduwa ta hanyar hada jiki. A cewarsa, a yi amfani da wasu hanyoyin yin musabaha da jama'a.

2. Banda hada jiki

Hakkin mallakar hoto Getty

Idan kuna tunanin wani na dauke da cutar Ebola, ka da ku taba shi. Abin babu dadi ga 'yan uwa. Amma kuma hada jiki ta yadda zufa ko amai ko yawu ko maniyi za su taba wani, hakan zai iya yada cutar Ebola.

Daga cikin hanyoyin gane cutar har da zazzabi, da kashe lakar jiki, da bushewar makoshi, da ciwon kai, da kuma yawan gajiya. Daga nan kuma sai mutum ya soma amai da zawo da kuma zubar da jini.

A shawarci wanda ya ji daya daga cikin wannan yanayin, ya tuntubi likita.

3. Guji Taba Gawa

Hakkin mallakar hoto Getty

Idan kana tunanin cutar Ebola ta kashe wani, to kada ku taba gawarsa, wajen yin jana'izarsa saboda za a iya kamuwa da cutar Ebola sakamakon taba gawar wanda cutar ta kashe.

Ku tuntubi tawagar ta musamman ta kwararrun kiwon lafiya domin su san matakan da za su dauka a kan gawar.

4. Daina cin namun daji

Hakkin mallakar hoto AFP

A guji farauta da cin namun daji irin su birai, da jemage , da sauransu saboda ana iya kamuwa da cutar ta wannan hanyar.

Ku tabbarda cewar an dafa abinci da kyau kafin a ci.

5. Kada a firgita

Hakkin mallakar hoto Getty

A daina yada jita-jita saboda hakan na kara jefa al'umma a cikin al'umma.

Idan har aka tuntubi jami'an kiwon lafiya sun san irin matakan da suka dace a dauka domin tabbatar da cewar cutar ba ta yadu tsakanin al'umma ba.