Ebola: kasashe za su bude iyakokinsu

Ma'aikatan lafiya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ma'aikatan lafiya

Ministocin lafiya na kasashen yammacin Afrika da suke taro a Ghana, sun amince da a dage matakin takaita zirga-zirga da aka dauka akan kasashen da annobar cutar Ebola ta afka wa.

Ministocin sun dauki wannan mataki ne sakamakon shawarar da hukumar lafiya ta duniya ta bayar, cewa takaita zirga-zirga ya haifar da karancin abinci da muhimman abubuwan, wanda hakan ta ce yana kawo nakasu ga kokarin yaki da cutar.

Hukumar ta ce maimakon takaita zirga-zirgar, kamata ya yi, kasashen da cutar ta fadawa, su rika gudanar da bincike kan lafiyar masu shiga da fita daga cikinsu.

Babban darektan hukumar lafiya ta kasashen yammacin Afrikan Xavier Crespin , ya ce manufar taron nasu ita ce, musayar fahimta da ilimi a tsakaninsu.

Hukumar lafiyar ta duniya ta yi gargadin cewa, fiye da mutane dubu 20 za su iya kamuwa ta cutar ta Ebola, kafin a iya magance ta.