Google ya kera jirgi marar matuki

Kamfanin Google yayi gwajin wani karamin jirgi sama mara matuki da ya kera, wanda za a iya amfani da shi wajen aikawa da sakonnin kayayyaki.

A reshen da ake gudanar da bincike na kamfanin, Google X, aka kera karamin jirgin, kuma a nan ne aka kera motar da kamfanin ya yi mai tuka kanta.

Reshen na Google X, ya shafe shekaru biyu yana aiki asirce, sai yanzu aka san da shi.

Kamfanin Google ya ce burinsa shi ne ya kera karamin jirgin sama mara matuki da za a iya amfani da shi a lokutan bala'o'i, ta hanyar yin amfani da shi wajen kai kayan agaji ga mutane.

Kamfanin ya ce jiragen za su iya daukan kananan kayayyaki, kamar magunguna da batura su kai wa mutanen da ba za a iya zuwa inda suke ba a wuraren da aka samu girgizar kasa, ko ambaliyar ruwa, da wuraren da suke fama da yanayi maras kyau.

Shugaban Google X, Astro Teller ya ce da daukar kaya kadan-kadan, jiragen za su cimma mutane da yawa a lokutan tsananin bukata.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jirgin zai iya tashi da sauka, kamar ungulu ba lallai sai ya sheka a guje ba.

Da farko, anyi shirin kera jirgin Google maras matuki ne da nufin aikawa da akwatin kayayyakin magani ga mutanen da ake zaton sun samu bugun zuciya.

Dalilin hakan kuwa shi ne, jiragen za su fi saurin kai akwatin kayan akan a tura su ta motar asibiti.

Wani jami'in Google X, Dave Voss ya ce ''idan aka samu na'urori irin wannan, za a iya amfani da su a wasu ayyukan da ke bukatar gaggawa, kuma su biya bukata''.

An yi maraba da wannan sabon jirgi a jahar Queensland da ke arewa maso gabashin Australia, a inda aka yi nasarar gwada aikewa da kayayyaki zuwa gonaki.

An zabi Australia ne domin gwajin jirgin saboda abin da kamfanin Google ya kira dokokin da suka yarda a yi amfani da jirage marassa matuka a nahiyar.

Hakkin mallakar hoto AP

Fadin jirgin na Google daga fukafuki zuwa fukafiki ya kai mita daya da rabi, kuma su na dauke da farfela guda hudu.

Nauyin jirgin, hadi da na kayan da yake dauke da shi, ya kai kilogram 10.

Sannan zai iya tsayawa cik a sama a wuri daya, kuma zai iya tafiya mai nisa sosai.

Haka zalika, da zarar an saita adireshin inda zai kai sakon, jirgin ya na sarrafa kanshi har zuwa inda zai je.

Wannan ya sa jirgin ya bambanta da sauran jirage marassa matuka na soji, wadanda ake sarrafasu da wata na'ura daga kasa.