Hama Amadou ya tsere zuwa Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Tun a makonnin da suka wuce aka tsare matar Hamma Amadou

Shugaban Majalisar Dokokin Niger, Hama Amadou wanda ake zargi da siyo jarirai daga Nigeria ya tsere zuwa Burkina Faso.

Rahotanni sun nuna cewar Hama Amadou ya gudu zuwa Ouagadougou ne bayan da wasu shugabannin majalisar dokokin kasar suka kada kuri'ar cire masa rigar kariya domin ya gurfana gaban kuliya bisa zargin da ake masa.

Wasu na kallon lamarin a matsayin bita da kullin siyasa saboda Amadou na daga cikin wadanda za su iya kalubalantar Shugaba Mahamadou Issoufou a zaben shekara ta 2016.

Wani dan majalisar dokokin Nigeria, Mohammed Ben Omar ya shaidawa BBC cewar sun amince a bada damar gudanar da bincike kan Hamma Amadou ne domin gaskiya ta yi halin ta.

Tuni dai bangaren Hama Amadou ya shigar da kara gaban kotu a kan cewar zaman da aka yi na cire masa rigar kariya haramtacce ne.

Jami'an tsaron Niger, sun damke mutane 17 ciki hadda matar Hamma Amadou da matar minista Abdou Labbo.