'Yan bindiga sun kai hari Bauchi a Nigeria

Image caption A baya dai 'yan kungiyar Boko Haram sun kai hari a jihar ta Bauchi

Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan karamin sansanin soji da ke jihar Bauchi a ranar Alhamis.

Rahotanni na cewa an yi musayar wuta da maharan da kuma sojoji, abin da ya kai ga mutuwar daya daga cikin 'yan bindigar.

Yayin da jami'an tsaro da dama kuma suka samu raunuka a lokacin harin.

Lamarin ya faru ne kwanaki kadan bayan an kashe wasu 'yan sanda uku a wani harin da aka kai a garin Toro da ke jihar ta Bauchi.

Karin bayani