An kashe akalla mutane 6 a rikicin Nassarawa

Hakkin mallakar hoto website nassarawa
Image caption Rikicin kabilancin ya yi sanadin jikkata mutane da dama da aka kwantar a asibiti

'Yan sanda a jihar Nassarawa sun tabbatar da mutuwar mutane shida sakamakon wani rikicin kabilanci tsakanin Fulani makiyaya da Manoma 'yan kabilar Eggon.

Wasu rahotanni sun ce rikicin wanda ya barke a ranar laraba, ya janyo mutuwar mutane da dama, tare da kone gidaje wadanda 'yan sanda suka ce adadinsu ya kai 46.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Nassara, ASP. Umar Isma'il wanda ya tabbatar da cewa an kone wasu mutane a rikicin, amma ba su san hakikanin mafarinsa ba ya zuwa yanzu.

Duka bangarorin biyu na Fulani da 'yan kabilar Eggon na cewa an kashe musu mutane da dama a rikicin wanda ya faro tun a makon jiya, yayin da mutane da dama suka kaurace wa yankunansu.