Ukraine: Merkel ta nemi bayani kan sabon farmaki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana zargin Rasha da kai sabon farmaki a Ukraine

Shugabar Jamus Angela Merkel ta bukaci bayani daga Shugaban Rasha Vladmir Putin bayan rahotannin dake cewa dakarun Rashan sun kaddamar da wani farmaki cikin kudu maso gabashin Ukraine.

UKraine tace dakarun na Rasha sun tsallaka kan iyaka kuma suna goyan bayan hare haren da 'yan aware ke kai mata.

Amurka ma tace tana tsammanin Rashan na shirya kai wani sabon farmaki a Ukraine.

Sai dai Rasha ta musanta cewa tana goyan bayan 'yan tawayen ko kuma basu makamai.

Daya daga cikin shugabannin dake goyan bayan masu tayarda kayar bayan Rashan Denis Pushlin ya fadawa wani Taron manema labarai cewa ba hannun Rasha a wannan farmaki.