An goge shari'u na cikin Internet a Amurka

Kotun Kolin Amurka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kotun Kolin Amurka

An goge dukkan wasu mashahuran shari'u na kare hakkin dan adam da daya daga cikin manyan alkalan Amurka ta jagoranta daga cikin Internet.

Hukumar dake kula da adana bayanan shari'u cikin na'ura mai kwakwalwa watau Komputa a Amurka da ake kira Pacer ta goge shari'u da dama da aka gudanar wadanda ake ganin ba su jeranta da sabuwar na'urar adana bayanan ba.

Wadannan shari'oi sun hada da daukaka karar da Mai shari'a Sonia Sotomayor ta saurara, gabanin nada ta a matsayin babbar mai shari'a ta kotun kolin Amurka.

Cikin shari'un kuma da aka goge, har da wata shahararriyar shari'a ta nuna wariyar launin fata.

Shari'ar Ricci da DeStefano wadda aka yi zargin cewa an yi la'akari da launin fata wajen karin girma ga ma'aikatan kwana-kwana na Connecticut tana daya daga cikin manyan shari'oi na Mai shari'a Sotomayor a lokacinda take shari'a a Kotun daukaka kara.

Shari'ar tana daya daga cikin shari'oi da dama da hukumar Pacer ta goge kwata-kwata daga kundin ajiya.

A wata sanarwa da ta bayar makonni biyu da suka gabata, hukumar Pacer ta ce, yanayin tsarin tafiyar da wasu kotuna biyar na nufin ba za a kara samun bayanan shar'ioinsu ba a cikin internet.

Mai shari'a Sotomoyor ta yi aiki da Kotunan daukaka kara na 2 daga shekarar 1998 zuwa 2009.

Duk da haka dai za a samu bayanan daga wadannan kotuna da ake magana a kan su, to sai dai za a caji dala 30 kafin a baiwa duk mai neman ganinsu ta internet.

Bugu da kari kuma za a dauki kwanaki kafin a samu bayanan da ba a sanya su cikin na'urar mai kwakwalwa ba.

Karin bayani