Cutar Ebola ta shiga kasar Senegal

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce ya kamata a dauki matakan da suka wajaba don rage yaduwar cutar Ebola

Mahukunta a kasar Senegal sun tabbatar da bullar cutar Ebola a karon farko a kasar.

Ministar lafiya ta kasar ta ce wani mutum ne ya shiga da kwayar cutar daga kasar Guinea.

Ta ce yanzu haka mutumin yana wani asibiti a Dakar babban birnin kasar.

A kasar Guinea, jami'an tsaro sun tarwatsa wata zanga-zanga kan jita-jitar cewa ma'aikatan kiwon lafiya na harbar mutane da kwayar cutar.

Kasar Senegal ita ce kasa ta biyar a Afirka ta Yamma da aka samu bullar cutar ta Ebola da ta hallaka mutane fiye da dubu daya da dari biyar.

Karin bayani