Nigeria ta maido da korarrun likitoci

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ministan Lafiya, Onyebuchi Chukwu

Gwamnatin Nigeria ta maido da likitoci masu neman kwarewa su 16,000 wadanda ta kora a tsakiyar wannan watan a lokacin suna yajin aiki.

Ma'aikatar Lafiyar kasar ta ce korarrun likitocin za su koma bakin aiki ne daga ranar Juma'ar nan.

Ministan Lafiya, Onyebuchi Chukwu wanda ya sanar da haka, ya umurci shugabannin manyan asibitocin gwamnati su mika wa likitoci masu neman kwarewa takardar shaidar ci gaba da neman gogewa a aikin likita.

A cikin makon da ya gabata ne kungiyar Likitocin kasar ta janye yajin aikinta, tare da sharadin cewar dole ne sai an dawo da likitoci masu neman kwarewa da gwamnati ta kora a bakin aikinsu.

Likitoci masu neman kwarewa su ne kashi 70 cikin 100 na likitocin da ake da su a Nigeria.