SAS: Ba na daukar nauyin Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau da mayakan kungiyar

Tsohon gwamnan Jihar Borno Sanata Ali Modu Sheriff, ya musanta zargin cewa yana daga masu daukar nauyin 'yan Boko Haram, da cewa ana son bata masa suna ne kawai.

Ya ce wasu mutane ne ke neman shafa masa kashin kaji kawai domin ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Tsohon Sanatan yana mayar da martani ne ga bayanin da wani dan kasar Australia, Stephen Davis, ya yi cewa wasu kwamandojin Boko Haram ne suka tabbatar masa da hakan.

Ali Shariff, ya ce wasu ne suka biya baturen domin ya bata masa suna kawai.

Kuma ya ce zai shigar da kara akan baturen a Ingila inda ya je ya bayyana wannan kazafi, maimakon tun yana Najeriya ya fada.

Shi dai Mr Davis, an ce yana shiga tsakani ne da 'yan Boko Haram da gwamnati domin ceto 'yan matan nan 'yan makarantar Chibok da 'yan Boko Haram suka sace.