Ebola: Likita ya kara mutuwa a Saliyo

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Saliyo a naga kasashen Yammacin Afrika hudu da cutar Ebola ta yi kamari

Rahotanni daga Saliyo sun ce an kara samun wani likita da ya mutu sakamakon kamuwa da cutar Ebola a kasar.

Likitan ya kamu da cutar ne lokacin da ya ke yi wa wasu da suke fama da ita magani.

Kawo yanzu, fiye da ma'aikatan lafiya 20 ne cutar ta kashe a kasar ta Saliyo, kuma yawancin ma'aikatan sun shiga yajin aiki saboda rashin biyan su kudaden alawus din su.

Tun da farko dai, kasar Liberia ta dage takunkumin killacewa da ta sanya akan wata unguwar talakawa sama da mako daya da ya gabata, don hana cigaba da yaduwar cutar.

Fiye da mutane 1500 ne cutar ta Ebola ta kashe a yammacin Afika tun bayan barkewarta a cikin watan Maris.

Karin bayani