Ecuador za ta bullo da kudi na zamani

Digital currency Ecuador Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sabon kudin zamani na intanet

Gwamnatin Ecuador, ta ce za ta kaddamar da nau'in kudi na zamani ( Digital Currency) da za a rinka hada-hada da shi ta intanet, irinsa na farko da wata kasa a duniya ta bullo da shi, a farkon watan Disamba mai zuwa.

Jami'an babban bankin kasar, suka ce kudin wanda har yanzu ba a sa ma sa suna ba, za a rikaamfani da shi ne kafada da kafada da dalar Amurka, kuma za a yi hakan ne , domin tallafa wa talakawa, wadanda ba sa iya hulda da bankuna.

Ana ganin bullo da wannan sabon nau'i na kudi zai iya kara yawan kudaden da ke hannun jama'a da kuma karya darajar dalar Amurka, da hakan wani mataki ne na daina amfani da dalar, wadda kasar ke amfani da ita tun shekara ta 2000, lokacin da bankunan kasar suka shiga matsalar kudi.