Taro kan rikicin kasar Ukraine

Ukraine Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ukraine

Ministocin harkokin kasashen waje na tarayyar Turai suna shirin tattauna a rana ta biyu akan rikicin kasar Ukraine, a birnin Milan na Italiya,

Ana sa ran shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenka zai gana da shugabbanin hukumar Turai watau Herman Van Rompuy da kuma Jose Manuel Barroso me barin gado kafin a soma taron.

Haka kuma ana sa ran Mr Poroshenko zai matsawa shugabbanin kassashen Turai daukar tsauraran matakai akan Rasha

A jiya juma'a ne ministan harkokin wajen Jamus Frank Steinmeir ya yi gargadin cewa rikicin Ukraine ya na neman faskara har ya gaggara magance wa.

Mr Steinmeir dai na magana ne akan rahotonin da suka ce sojojin Rasha sun shiga cikin Ukraine inda suka karbe iko a wani gari a yankin kudu maso gabashin Ukraine

Mutane fiye da dubu biyu ne suka rasa rayukansu a yankin Donesk da kuma Luhansk tun bayan barkewar rikicin