An yi na'urar buga takarda mai tafiya

Hakkin mallakar hoto fujixerox
Image caption An tsara na'urar ta yadda ba za ta taba karo da wani abu ba a inda ke aiki da ita

Kamfanin Fuji Xerox ya kirkiro naurar buga rubutu da za ta rika tafiya ta kaiwa wanda ya buga takardu har teburinshi domin ya dauka.

Hakan na nufin ba sai mutum ya tashi daga inda yake zaune ba, ya je wajen na'urar ya dauko takardun da ya tura mata ta buga ba.

Na'urar za ta rika yawo ne a ko ina a cikin ofis, inda duk mutumin da ya tura mata rubutu , za ta buga kuma ta zo har teburin da yake ya dauka.

An tsara na'urar ne domin aiki a wuraren jama'a domin alkinta takardun sirri.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Nau'in wata na'urar buga rubutu da zane-zane

Maganadisun da ke jikin na'urar zai sa ta san inda mutum ko wani abu da ke kan hanya yake domin ta kauce masa ka da ta yi karo da shi.

Kamfanin Fuji Xerox da ya kirkiro na'urar, wanda hadaka ce ta kamfanoni biyu, yana gwada aikin na'urar a watannan a wani babban ofis a Tokyo.

Sai dai kuma wasu na ganin fasahar ba za ta kawo saukin kashe kudi ba idan aka yi la'akri da yadda wasu na'urorin na buga takardu suke.

Wata kwararriya akan harkar Maggie Tan na ganin tuni daman akwai wasu na'urorin da suka fi wannan saukin aiki.