Somalia: Gagarumin hari a kan Al Shabbab

Sojojin gwamnatin Somalia Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojojin gwamnatin Somalia

Mahukuntan kasar Somalia sun ce dakarunsu da wadanda takwarorinsu na Tarayyar Afirka ke marawa baya sun kaddamar da farmaki kan kungiyar mayakan Islama na al Shabab a yankin kudancin kasar.

Sun yi hakan ne da nufin kwace garuruwan Buulo Mareer da Baraa-wet-wo dake yankin Shabelle inda kungiyar ta Al Shabab tafi karfi.

A halin da ake ciki sojojin gwamnati sun kashe 'yan tawayen 15 sun kuma kwace garin Buulo Mareer

Gwamnan lardin Shabelle Abdukadir Mohamed Nur, ya ce dakarun gwamnati na namijin kokari a farmakin da suka fara ranar Jumma'a.

Wani Jami'in gwamnati yace sojojin suna kokarin sake kwace garin Baraa-wet-wo a yankin Shabelle daga hannun 'yan tawayen.

Karin bayani