Sojojin Iraqi sun shiga garin Amerli

Hakkin mallakar hoto

Sojojin hadin guiwa da suka hada da dakarun Iraqi, da na mayakan Shi'a da na Kurdawa peshmerga, sun shiga garin Amerli, inda mayakan kasar musulunci suka kewaye mazauna yankin har na tsawon watanni biyu.

Jiragen Iraqi da Amurka ne ke basu kariya ta sama.

Amurka ta ce tana kan jefa taimakon kayan abinci ga mazaune garin, yayinda ake kai harin ta sama

A baya bayan na ne Pira ministan Australia Tony Abbott, ya amince kasarsa ta zama daya daga cikin kasashe da dama masu kai agajin ta sama.

Ya ce "Australia ta amince ta shiga cikin aikin kai agajin kayan yaki ta sama ga mayakan Kurdawa.

Karin bayani