Matasa sun gudu daga Gamborun Ngala

Najeriya Boko Haram Hakkin mallakar hoto AFP PHOTO BOKO HARAM
Image caption Najeriya Boko Haram

A Najeriya matasa masu shekaru 15 zuwa 20 sun tsere daga Gamborun Ngala a jahar Borno bayan harin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai hari.

Matasan sun ce sun yi hakan ne saboda fargabar da suke da ita na tilasta masu daukar makamai da 'yan kungiyar ke yi ko kuma hallakasu.

Rahotannin sun ce 'yan kungiyar ta Boko Haram sun kashe mutane dama a garin.

Da farko 'yan Boko Haram sun cewa mazauna garin za su iya zama kuma ba zasu taba su ba, sai dai daga bisani suka sauya shawara

Tun a makon da ya gabata ne 'yan Boko Haram din suka kama garin na Gamborun Ngala a yunkurinsu na kafa daular musulunci.