Mutane fiye da 200 sun jikkata a Pakistan

Wasu da suka jikkata a Pakistan Hakkin mallakar hoto
Image caption Wasu da suka jikkata a Pakistan

Wani dauki ba dadi tsakanin 'yan sanda da masu zanga zangar kin jini gwamnati a Pakistan a daren da ya gabata ya yi sanadiyyar jikkata mutane sama da 250 ,galibinsu 'yan sanda.

Rikicin ya faru ne bayan masu zanga zangar da ke neman Frai minista Nawaz Shariff ya yi murabus, sun yi maci zuwa gidan sa a Islamabad, da motar janwe domin kawar da shingayen da 'yan sandan suka girka...

Shugaban 'yan sanda a Islamabad ya shaidawa BBC cewa an kama masu zanga zanga kusan dari kuma a cewarsa da dama daga cikinsu na rike ne da aduna da kuma wasu miyagun makamai.

Sai dai malamin adinin musulunci wanda yana cikin 'yan adawa dake jogorantar zanga zangar Tahir ul Qadri ya yi Allah wadai akan matakin da yan sanda suka dauka kuma ya musanta zargin cewa suna rike da makamai

Manyan asibitoci a birnin Islamabad sun shaidawa BBC cewa mutane 264 ne suka ji raunuka ciki har da 'yan sanda 26.