Putin ya yi kiran tattaunawa kan Ukraine

Shugaban Rasha Vladimir Putin Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Rasha Vladimir Putin

Shugaban Putin na Rasha yayi kiran tattaunawar gaggawa kan matsayin gabashin Ukraine a wani bangare na sasanta kawo karshen rikicin dake faruwa a yankin.

Hakan na zuwa ne kwana guda gabanin tattaunawar da za a yi a Minsk, tsakanin kasashen Ukraine, da Rashar da kungiyar Tarayyar Turai kan rikicin.

Ta wani gefen kuma Kasashen Rashar da Ukraine sun yi musayar fursunoni, inda Ukraine ta mika ta mika sojojin lema 10, yayinda Rasha ta mika sojojin Ukraine 63.

Mataimakin kwamandan rundunar sojin saman kasar Rasha General Alexei Ragozin, ya ce za a duba lafiyar sojojin lemarsu da suka dawo.

Ya kara da cewa "sasantawar ta kasance mai wahalar gaske amma kuma daga karshe komai ya tafi daidai, abu mafi muhimmanci shine sojojinmu sun dawo".

Karin bayani