Karin dubban mutane sun yi zanga zanga a Hong Kong

Zanga zangar Hong Kong Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zanga zangar Hong Kong

Karin wasu duban mutane sun shiga cikin zanga-zangar kare mulkin dimokradiyya a Hong Kong a jajiberin ranar mulkin kai ta kasar da ake sa ran gudanar da gagarumin gangami.

Cincirundon jama'ar da suka mamaye tsakiyar birnin da sauran manyan hanyoyi sun karu zuwa duban daruruwa yayinda dare ke kara gabatowa.

Ana ta raira waken shugaban yankin na Hong Kong ya yi murabus, wanda a baya yayi kira ga taron da su watse.

A kalamansa na farko shugaban kasar China, Xi Jinping, ya ce China za ta kare martaba da ci gaban Hong Kong.