Iyalan Rockfeller za su zuba jari a sabon makamashi

Hedikwatar gidauniyar Rockfeller

Iyalan Rockefeller hamshakan attajiran nan da suka yi tashen kudi daga kamfanonin mai sun ce kungiyarsu ta miliyoyin daloli mai taimakon al'umma tana shirin sauya zuba jari daga harkar makamashi mai fidda hayaki zuwa fannin makamashi marar gurbata yanayi.

Gidauniyar 'yan uwa ta Rockefeller ta fada a wani taron manema labarai a birnin New York gabanin taron kolin Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi cewa sun yi alkawarin sayar da wata kadarar su da ta danganci makamashi mai fidda hayaki ta tsabar kudi fiye da dala biliyan hamsin.

Shugaban wata kungiyar kare muhalli mai suna E3G kuma tsohon mai baiwa gwamnatin Birtaniya shawara kan sauyin yanayi Tom Burke yace zamanin makamashi mai fidda hayaki ya riga ya wuce.

"Ya ce,wannan lokaci ne muhimmi, musamman sanarwar da Rockefeller suka bayar na zamanin makamashin mai.

A yanzu kuma sun sanar da karshen zamanin makamashin na mai kuma wannan abu ne mai fa'ida ga makomar duniya."