Gargadi kan dumamar yanayi

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Hayakin jiragen sama shi ne mafi saurin haddasa dumamar yanayi

Masana a Birtania sun yi gargadin cewa, za a iya kasa cimma burin rage yawan hayaki da ke sa dumamar yanayi, idan yawan nonon dabbobi da kayan da ake yi da shi na abinci da naman da mutane ke ci ya karu kan yadda yake a yanzu.

Binciken ya kiyasta cewa, yawan hayakin da ake fitarwa a sanadiyyar girki da suran hanyoyin samar da abinci zai karu da kashi 80 cikin dari nan da shekara ta 2050.

Sai dai rahoton ya ce, za a iya sauya wannan yanayi ko rage hadarin hakan, idan aka bunkasa hanyoyin noma a kasashe masu tasowa, da rage bannar abinci kuma mutane su rage yawan naman da suke ci.