Mali: Gwamnati za ta gana da 'yan tawaye

Image caption Wasu daga cikin 'yan tawayen Mali

A yau ne gwamnatin Mali za ta tattauna da wakilan kungiyar 'yan aware daga yankin arewa domin shawo kan fadae-fadacen kasar.

Tun bayan da kasar ta koma kan tsarin dimokradiyya shekara daya da ta wuce take fama da rikici.

Za a gudanar da tattaunawar ne, wadda ita ce kusan ta biyu a baya-bayan nan, a Algiers babban birnin kasar Algeria mai makwabtaka da Malin.

Za a yi taron a Algeria ne, saboda mafaka da goyon bayan da ake gani Abzinawa 'yan tawaye suke samu daga kasar a kudanci.

Wata matsala da ake gani da ke kawo cikas ga shirin sasantawar, ita ce, su kansu 'yan tawayen na Abzinawa sun rarrabu.