Amnesty na binciken cin zarafi a Iraqi

Mayakan ISIS Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Myakan na ISIS dai sun hallaka 'yan kabilar Yazidi tsiraru a kasar ta Iraqi.

Kungiyar nan mai fafutukar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International tace ta tattara hujjoji dake nuna cewa mayakan ISIS sun yi ta kaddamar da abinda ta kira kisan kabilanci a arewacin Iraqi.

Rahotan yace mayakan na aikata laifukan Yaki da suka hada da kisa da kuma sace mutanen da suka fito daga tsirarun kabilu da sauran mabiya addinai.

Kungiyar tace yawanci kashe- kashen da aka yi, sun auku ne a lardin Sinjar a watan Agusta.

Duncan Spinner shi ne shugaban Hukumar a kasar Iraqi, ya bayyana cewa gwamnatin kasar ce ta bukaci da su gudanar da bincike a kaburburan da aka binne mutane da dama a cikinsu, idan an samu sararin yin hakan.

Ya kuma kara da cewa a sansanin Speicher da ke kusa da yankin Tikrit an samu kaburarin da mayakan ISIS suka binne mutanen da suka hallaka kusan 800 zuwa 1700.

Mazauna yankin kuwa sun sun ce sun yi amanna da cewar mayakan ISIS din sun hallaka akalla mutane 400.