'Yan Bama na tserewa zuwa Maiduguri

Mazauna garin Bama na guduwa zuwa Maiduguri da kafafunsu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mazauna garin Bama na guduwa zuwa Maiduguri da kafafunsu

A Najeriya, rahotanni daga garin Bama na jahar Borno da ke arewa-maso-gabashin kasar na cewa 'yan bindiga sun kwace iko da garin na Bama, bayan an shafe tsawon wunin jiya ana fafatawa tsakanin wasu da ake zargin cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne da kuma sojojin Najeriya.

Wannan dai ya tilastawa dubun dubatar mazauna garin na Bama kaura zuwa birnin Maiduguri.

Wasu dai sun yi tafiyar kafa ne daga Bama zuwa Maidugurin, wanda keda tazarar kilomita saba'in a tsakaninsu.

Hedikwatar Tsaron Najeriya ta bayyana cewa ba zata iya bayyana yawan mutanen da rikicin Baman ya rutsa da su ba.

Amma tace za a yi duk abinda ya zama wajibi domin a murkushe 'yan Ta'adda.