Sojoji sun fatattaki 'yan Boko Haram

Sojojin Nijeriya a bakin aiki. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojin Najeriya na ci gaba da fafatawa da mayakn na Boko Haram da suka mamaye wasu yankuna na jihar Borno.

Rundunar Sojin Najeriya tace ta kashe mayakan Boko Haram kusan saba'in a lokacin wani hari da mayakan suka kai a garin Bama dake arewa maso gabashin Kasar.

Jami'ai sunce 'yan tawayen sun shigo garin ne da sanyin safiyar Litinin a cikin tankokin yaki da kuma manyan motoci.

Rahotanni daga yankin sunce sojojin gwamnati sun fatattaki 'yan bindigar

Mazauna garin Baman da dama dai sun tsere zuwa birnin Maiduguri wanda keda nisan kilomita 70 da garin.

Mayakan kungiyar Boko Haram dai sun mamaye wasu daga cikin yankunan jihar Borno da suka hada da Gwoza, da Dambua, da Dikwa da kuma Gamborou Ngala.

Sai dai gwamnatin Najeriya da jami'an tsaro sun ce su na fafatawa da mayakan domin dakile tada kayar bayan da Boko Haram ke yi a arewacin kasar.