Hama Amadou ya gudu Belgium

Hakkin mallakar hoto
Image caption Hama Amadou ya ce zargin nada nasaba da siyasa

Wasu rahotannin kafafen yada labarai a Niger na nuna cewa, shugaban majalisar dokokon kasar, Malam Hama Amadou yanzu haka na kasar Belgium.

Tun a makon jiya ne Malam Hama Amadoun ya fice daga kasar ta Niger ya shiga Burkina Fasso, bayan da wani kwamitin majalisar dokokin kasar yayi zama ya zartar da matakjin cire masa rigar kariyar da yake da ita.

Matakin majalisar zai bada damar gurfana Hama Amadou gaban shari'a domin kare kansa daga zargin hannu a safara jarirai daga Nigeria zuwa Niger.

Shi dai Hama Amadou na zargin cewa akwai siyasa cikin wannan lamari, wanda yayi sanadiyar mai dakinsa na ci gaba da zama a tsare tare da wasu mutanen kimanin sha shida tun cikin watan Yuni.

Jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulkin Niger ta ce ba za ta dauki wani mataki a kan batun ba har sai kotun tsarin mulkin ta yanke hukunci game da batun cirewa Hama Amadou rigar kariya.

Karin bayani