Masu kwasar bahaya a Indiya

Masu kwasar bahaya a Indiya

Gangashree
Bayanan hoto,

Miliyoyin al'ummar talakawa ne ke aikin kwashe bahaya da kwando daga Salga ta gargajiya, sannan su je su zubar. Mata kamar Gangashree wadda ta fito daga kauyen Kasela da ke arewacin jihar Uttar Pardesh na kwashe bahaya a gidaje. Tana diban bahayan a kwando sannan ta kai wajen gari.

Bayanan hoto,

Wannan sana'a da aka kwashe shekara da shekaru ana yi ya zama ruwan dare a kauyen Kasela, inda ake kallon masu yinta a matsayin wadanda ba a iya yi musu komai. Wannan matar ta shiga wani gida ta kofar baya domin kwashe bahaya a bandakunansu.

Bayanan hoto,

Manisha da ke zaune a gundumar Mainpuri a jihar Uttar Pradesh na kwashe bahaya a bandakunan gidaje 20 a kullum. "Ina amfani da faranti da aka yi da gwangwani da kuma tsintsiya wajen kwashe bahaya daga Shadda, sannan na tafi da shi na zubar. Aiki ne na kazanta sai na ji ba na son cin abinci." In ji Manisha.

Bayanan hoto,

Munnidevi da ke gundumar Etah ta ce ba ta samun kudi ta hanyar wannan sana'a. "Wani lokaci bai fi su ba da biredi guda biyu ba, wani lokaci ma daya. Wani gida ma ba su bani komai ba a cikin kwanaki biyu ko uku sai na daina zuwa. Sai suka zo suka yi mini barazana cewa idan ban koma ba, ba za su barni na zauna a inda nake ba, kuma ina zan samu abincin da zan ba dabbobi na? Muna da Shanu hudu, saboda haka dole na koma na kwashe musu salgar. "

Bayanan hoto,

"Majalisar kauyen Panchayat na daukar masu kwadago domin yin aikin samar da ruwa da akawu da kwashe shara da kuma wannan aikin da na ke yi na kwashe bahaya" A cewar Anil wanda ke gundumar Dhule. Ya kara da cewa idan dai ka fito daga al'umar Mehatar marasa galihu to ya zama dole ka yi kwasar bahaya.

Bayanan hoto,

"Majalisar kauye ce ta kawo iyali na nan domin mu kwashe bahaya a bandakuna na gargajiya da na zamani da kuma bahayan da ake yi a waje. Duk na kwashe na zubar a wani wuri. A gaskiya mun fi son mu koma gida ba ma son zaman nan." In ji Rajubai "Saboda aikin ya fara shafar lafiyata."

Bayanan hoto,

Wata kungiya mai fafutukar kare irin wadannan mutane, Rashtriya Garima Abhiyan ta kaddamar da wani kamfe domin 'yanto mutane 11,000 da ke aikin kwasar bahaya a jihar Madhya Pradesh.

Bayanan hoto,

Rekhabai ta ce lokacin da ta yi yunkurin barin aikin an yi mata barazana. "Daya daga cikin wadanda na ke yi wa aiki ya ce idan na sake zuwa gonarsa zai yanke kafafuwana.

Bayanan hoto,

Sahina ta fito ne daga gundumar Ujjain a jihar Madhya Pradesh ta bayyana cewa "Ana kebe ni wajen cin abinci a makaranta. Wata rana da abin ya ishe ni sai na zubar da abincin. Hakan ya sa aka rage mini maki saboda na nuna adawa da abin da ake yi mini."

Bayanan hoto,

Rahul wanda shi ma ya fito ne daga iyalan da ke aikin kwasar bahayan ya ce an dake shi saboda ya taba kwanon wani yaro dan masu da shi. Ya kara da cewa yaron aka sa ya yi masa bulala biyar a baya.

Bayanan hoto,

Wanda ya kafa kungiyar da ke fafutukar kwato 'yancin wadanda ke aikin kazantar, Ashif Shaikh ya ce " Kwashe bahayan mutane ba aiki ba ne, rashin adalci ne mai kama da bauta da kuma nuna wariya."

Bayanan hoto,

Senajbi ta daina kwasar bahaya a shekarar 2008 da taimakon kungiyar masu fafutukar kuma an zabe ta a matsayin mai wakiltar matan kauyensu.

Bayanan hoto,

Ta ce shekaru goma bayan sun daina kwasar bahaya, a yanzu suna da masunta kuma gwamnati ta amince su yi kamun kifi a wannan tafkin.