A ina kungiyar IS ke samun tallafi?

Mayakan IS

Ana dai zargin wasu kasashen yankin Gulf da tallafawa kungiyar IS da ke Iraqi da kuma Syria.

An yi rubuce-rubuce da dama akan batun irin tallafin da kungiyar ke samu musamman daga kasashen yankin Gulf.

Yawanci an fi zargin kasashen da suka hadar da Qatar da Turkiyya da kuma Saudi Arabia da taimakawa kungiyar wajen tsayawa da kafar ta.

Sai dai kuma a gaskiya wannan batu ne mai sarkakkiya.

Ko shakka babu akwai wasu masu kudi daga wadannan kasashe da ke tallafawa kungiyar ta IS da kudade a Syria, yawancinsu kan cika jaka da kudi su tafi zuwa Turkiyya sannan da sun isa sai su mika wannan jaka dauke da miliyoyin daloli ga wadannan mutane.

Wannan lamari ne da ya faru a shekarun 2012 da 2013, amma daga wancan lokaci abubuwa sun lafa, a yanzu kudaden shigar da da kungiyar ke samu kalilan ne ke zuwa daga wadannan kasashe na yankin Gulf.

Hakkin mallakar hoto reuters

Kasashen Saudi Arabia da Qatar sun yi amannar cewa, nan ba da jimawa ba gwamnatin shugaba Bashar al-Assad ta kusa rushewa, kuma zasu iya cimma manufofin su ne ta hanyar kungiyoyin mayaka mabiya Sunni a kasar.

A bangarenta kasar Turkiyya tana gudanar da wani tsari ne na kula da kan iyakoki wanda yake cike da alamomin tambaya saboda ana shiga da makamai da kuma kudade cikin Syria tare da goyon bayan Qatar da Saudiyya.

Kowa dai ya yi tunanin cewa hakan zai taimaka wajen kawo karshen mulkin shugaba Assad, da kuma sake mayar da Syria karkashin mulkin 'yan Sunni, sannan zai kuma karya dangantakar da ke tsakanin 'yan Shi'ar Iran da kuma gwamnatin Syria.

Yawancin wadanda ke goyon bayan wannan manufa tuni suka shiga cikin Syria kuma sun yi yaki sun mutu duk a dalilin goyon bayan kungiyar ta IS.

Kungiyar ta IS ta kafa wani abu mai kama da cikakken tsarin gwamnatin kasa kamar ma'aikatu da kotuna da kuma tsarin karbar haraji wanda mutanen yankin da suke, ke biyan haraji kadan kasa da wanda al'ummar Syria karkashin gwamnatin shugaba Assad ke biya.

Kungiyar tana kuma kafa tsari guda ne tun lokacin da ta fara karfin iko da yankunan da ta mamaye a farkon shekarar 2013.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba