Sojojin Amurka sun kaiwa Al-Shabab farmaki

Hakkin mallakar hoto n
Image caption Mayakan Al Shabab na yaki da gwamnatin Somalia

Ma'aikatar Tsaro ta Pentagon tace sojojin Amurka sun kaddamar da farmaki akan mayakan Al Shabab a Somalia.

Mai magana da Yawun Pentagon Rear Admiral Kirby yace ma'aikatar na nazarin sakamakon farmakin da sojojin suka kai, kafin fitar da karin bayanai

Al Shabab dai a yanzu na gudanar da yakar gwamnatin Somalia da kuma dakarun kassahen duniya dake goyawa gwamnatin baya