Amerika ta kai hari kan jagoran Al Shabab

Kungiyar Al Shabab Hakkin mallakar hoto afp

Ma'aikatar tsaron Amurka ta ce ta hari shugaban kungiyar 'yan gwagwarmayar Islama ta Al-Shabab ta Somalia, a wani hari da jirgin sama marar matuki.

Wani kakakin ma'aikatar ya ce ba a sani ba dai ko ya Allah an samu Ahmed Abdi Godane, to amma ya kara da cewa mutuwarsa za ta kasance a matsayin wani babban koma baya ga kungiyar.

'Yan kungiyar ta sa sun tabbatar cewar Godane na a cikin daya daga cikin motocin da aka sama a harin na daren jiya litinin.

Wani mai aiko wa BBC rahotanni a Somaliar ya ce an kai dakarun Amurka ta jirage masu saukar ungulu domin daukar gawarwakin wadanda aka kashe.

Godane ya yi fada a Afghanistan kafin komawarsa Somalia, inda ya mayar da Al Shabab daga wata kungiyar cikin gida ya zuwa wata barazana ga yankin sannan kuma wani bangare mai karfi na kungiyar Alka'ida.