Amurka ta damu da kisan dan Jarida

Dan jaridar Amurka Steven Sottloff da ISIS ta hallaka Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Steven Sotloff shi ne dan jarida na biyu dan asalin Amurka da mayakan ISIS suka hallaka.

Hukumomin Amurka sun ce idan an tabbatar da sahihancin hoton bidiyo na yadda aka yi wa Ba'amurke na biyu kisan gilla,hakan zai yi musu ciwo.

Kungiyar da ke fafatukar kafa daular musulunci wato ISIS ta yi gargadin cewa za ta hallaka wani dan jarida Ba'amurke idan Amurka ta ki daina kai wa mayakanta hare-hare ta sama a Iraqi.

Bidiyon dai ya na nuna gazawar Amurka wajen ceto 'yan kasar da masu ta da kayar bayan ke garkuwa da su, kuma babu alamun kasashen da Amurka ta nemi taimakawa game da sako wadanda aka yi garkuwa da su na da wani katabus a kan ISIS.

Haka kuma wannan bidiyon zai kara matsawa shugaba Obama lamba ta kai wa masu ta da kayar baya farmaki a sansaninsu da yake Syria.

Kakakin fadar White House, Yan Saki ta ce sare kan dan jarida na farko, James Foley da mayakan ISIS suka yi ya karfafa yunkurin da gwamnatin Obama ke yi wajen kirkirar kawancen kasasahen duniya, domin tunkarar mayakan ISIS, kuma mai yiwu wa ma a kara fadada shi.