'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda a Bauchi

Image caption Bayanai sun ce an tura karin jami'an tsaro zuwa Wukari

Hukumomi a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Nigeria sun ce 'yan bindiga da ba a tantance ko su wane ne ba, sun kai hari kan wani kamfanin hakar ma'adanai na 'yan kasar China, inda suka kashe jami'an 'yan sanda biyu da ke aiki a kamfanin.

Kakakin rundunar 'yan-sandan jihar ta Bauchi, DSP Haruna Muhammad, ya tabbatar wa BBC kai harin, wanda shi ne hari na uku da ya rutsa da jami'an tsaro a jihar cikin kimanin mako guda.

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin da dare yayin da jami'an tsaron ke aikinsu na gadi a kamfanin da ke kauyen Panshanu a karamar hukumar Toro.

Jihar Bauchi na daga cikin jihohin da 'yan Boko Haram ke kaddamar da hare-hare a kan jami'an tsaro da kuma gine-ginen gwamnati.