Boko Haram ta kwace karin garuruwa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan Boko Haram sun kafa totoci a garuruwan da suka kwace

Rahotanni daga garin Banki na jihar Borno a Nigeria na cewa da dama daga cikin mazauna garin sun tsere bayan da 'yan boko haram suka kai musu hari.

Bayanai sun ce a yanzu garin na karkashin ikon Boko Haram.

A halin yanzu galibin mazauna garin Banki din sun tsere ne zuwa wasu garuruwa da ke cikin kasar Kamaru.

Wannan lamari dai na zuwa ne a daidai lokacin da jama'a da dama ke tururuwa zuwa Maiduguri daga garin Bama, duk da cewa hukumomin jihar Borno na musanta cewa Boko haram sun kwace garin baki dayansa.

Bayanai sun nuna cewar a yanzu haka sarakunan gargajiya da dama a jihar Borno sun tsere daga garuruwansu saboda 'yan Boko Haram ne ke iko da yankunan.

Garuruwan Marte, Gamboru Ngala, Dikwa, Bama, Gwoza da kuma Damboa a yanzu duk suna karkashin Boko Haram.

'Yan gudun-hijira

Wani sabon rahoton da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, UNCHR ta fitar ya ce a yanzu yawan 'yan gudun hijirar Nigeria da ke Kamaru zai kai 39,000. A cewar hukumar ta yi wa mutane 20,000 rajista kawo yanzu.

Hukumar ta ce hare-haren kungiyar Boko Haram na baya baya su ne suka sa dubban mutane tserewa daga gidajensu domin neman mafaka.

A halin da ake ciki ana cewa akwai mutane kimanin kusan dubu dari shida da arba'in da biyar da suka tsere daga muhallansu a cikin Nigeria.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service