'Yan Boko Haram sun kwace garin Bama

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko Haram na kokarin kwace kauyukan da ke kusa da Kamaru

Rahotanni daga garin Bama na jihar Borno sun nuna cewa 'yan Boko Haram sun kwace iko da garin bayan musayar wuta da jami'an tsaron Nigeria.

Bayanai sun nuna cewar da farko lokacin da 'yan Boko Haram suka nemi shiga Bama dauke da makamai sun fuskanci turjiya daga jami'an tsaron Nigeria, daga bisani suka dawo suka diran ma garin suka samu 'galaba'.

Lamarin ya tilasta wa dubban mutane gudu zuwa Maiduguri babban birnin jihar Borno domin tsira da ransu.

Rundunar tsaron Nigeria ta ce tana kokarin dakile harin kamar yadda ta bayyana a shafinta na Twitter, sai dai kawo yanzu bayanai sun nuna akasin haka.

Cikin kusan wata guda, kungiyar Boko Haram ta karbe iko da garuruwa da dama da ke kan iyakar Nigeria da Jamhuriyar Kamaru.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar dubban mutane musamman a arewacin Nigeria.