Hukumomi sun musanta kwace garin Bama

Bama da wasu garuruwa a jahar Borno

A Najeriya, gwamnatin jihar Borno da ke arewa-maso-gabashin kasar ta musanta cewa baki-dayan garin Bama ya fada hannun 'yan kungiyar Boko Haram.

Gwamnatin ta ce 'yan kungiyar ta Boko Haram sun yi yunkurin kwace garin, a ranar Litinin, amma ba su yi nasara ba, inda ta ce yanzu haka ana cigaba da dauki-ba-dadi tsakanin 'yan kungiyar da sojojin kasar.

Haka kuma, wasu bayanai da BBC ta samu daga jami'an tsaro na nuna cewa, sojojin Najeriya na kara nausawa a kokarinsu na kwato garin na Bama daga hannun 'yan Boko Haram.

Garin Banki

Wani gari na baya-bayan nan da ke kan iyakar Nigeria da Kamaru, wato Banki ya shiga hannun 'yan Boko Haram.

Mazauna garin Banki sun shaida wa BBC cewa mayakan sun shigo garin abin da ya sa mazauna garin tserewa cikin daji da kuma shiga cikin kasar Kamaru.

Wani dan majalisar dattawa a yankin, Sanata Ahmad Zanna ya tabbatar wa da BBC cewa shi ma labarin da yake samu na tabbatar masa da kwace garin na Banki.