Najeriya ta nemi magance Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An yi taro a Abuja Nigeria domin warware matsalar Boko Haram

Hukumomin Nigeria da kasashe makwabtanta sun yi kira ga kasashen duniya su kara ba su gudunmawa a yunkurin dakile hanyoyin da kungiyar Boko haram ke samun makamai, da kuma kudade, yayinda ake ci gaba da nuna damuwa kan yadda kungiyar ke kara kame wurare.

Kiran na zuwa yayinda wasu rahotanni ke cewa 'yan Boko Haram din sun sake kama wani gari.

An ambaci ministan harkokin wajen Nigeria, Ambasada Aminu Wali, yana cewa takwarorin aikinsa daga kasar Benin, da Chadi da Kamaru da Nijar duk sun amince cewa akwai bukatar kara hada gwiwa a kokarin hana fasakwaurin makamai.