Borno:Shehu El-kanami ya kira a yi Azumi

Dangane da hare-hare da kuma kame garuruwa da kungiyar Boko Haram ke yi a jihar Borno, mai martaba Shehun Borno Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi ya yi kira ga al'ummar Musulmi da su fara azumin kwanaki uku daga gobe Alhamis don rokon Allah ya kawo karshen lamarin.

A wata sanarwa da aka aike wa BBC dauke da sa hannun sakataren masarautar Zanna Laisu Kazalma, Shehun na Borno ya kuma yi kira ga al'ummar Musulmi gaba daya da su yi ta addu'oi a dukkan masallatai a tsawon ranakun azumin.

Shehun har wa yau ya bukaci Musulmi a ko ina suke da su yawaita sadaka da taimako ga musakai da mabukata, musamman wadanda suka rasa matsgunansu ko suka gujewa rikicin Boko haram a koina suke.

A bangaren kiristoci kuwa, Shehun na Borno ya bukace su da su ma su ci gaba da addu'oin da suke yi na samun zaman lafiya a jihar Borno da ma Najeriya gaba daya.

Karin bayani