Sakon Twitter zai kai wani mutum Jarun.

Tambarin shafin Twitter Hakkin mallakar hoto
Image caption Za a yankewa Mr Nunn hukunci a karshen watan Satumbar nan.

An samu wani mutumi da laifin aikewa wata 'yar Majalisar Dokokin Amurka sakon batsa a shafin Twitter, saboda ta nuna goyon bayan ta ga masu fafautukar kare 'yancin mata.

An samu sakwannin Twitter mai cike da kalaman batsa da Peter Nunn mai shekaru 33ya aikewa Miss Stella Creasy 'yar jam'iyyar Labour mai wakiltar yankin Walthamstow.

Sai dai Mr Nunn ya musanta wanann zargi da ake masa, inda yace shi ba da wata manufa ya wallafa sakon ba.

Alkalin da ke sauraren shari'ar ta ce tabbas ba ta tantama sakwannin da aka wallafa su na cike ne da batanci.

Daya daga cikin sakwannin da aka wallafa dai na cewa ''Hanya mafi inganci da ka yi wa Mayya Fyade.''

Wani sakon kuma na cewa ''Idan ba za ka yi wa sananniyar mace barazanar yi mata fyade ba, to me kake yi da ita?''

Sai dai Mr Nunn ya ce duka sakwannin da ya ke wallafawa a shafin na sa na Twitter ya na yi ne kawai dan nishadi '' Wasa ne kawai, abin ne ya zo kaina a daidai lokacinm sai na yi tunanin abin dariya ne.''

Mr Nunn ya kara da cewa sakwannin barazana da yake aikewa Mis Creasy ba wai ya na nufin zai yi mata Fyade ba ne, a wani bangare ma kamar ya na nuna goyon bayan shi ne gare ta.

Za dai a yankewa Mr Peter Nunn hukunci a ranar 29 ga watan Satumba, haka kuma masu shigar da kara sun ce za su karbi oda daga kotu domin katange shi daga tuntubar Mis Creasy ta kowacce hanya.